Series

  • Dan Birni
    2 seasons

    Dan Birni

    2 seasons

    Bosho mutum ne wanda yayi yawon duniya wanda kuma a salonsa na barkwanci yake kokarin kawowa mutanen kauyensu hanyoyin ci gaba. Kwarai anan ya fara fuskantar adawa musamman ta wajen babban abokinsa Nagodi.

  • Matasa360 (Youth Variety Show)

    9 seasons

    Shirin Matasa@360 yana tabo al’adun matasa a wannan zamani, Shirin na ‘yan zamani yana kawo bangarori daban-daban kan ma’anar kasancewar mutum matashi a duniyar da ake magana da Harshen Hausa. Kama daga sana’o’i da warware matsaloli, zuwa sabbin kade-kade, da kwalliya da abubuwan da ake yayi, mat...

  • Akushi Da Rufi (The Tastiest Northern Nigerian Dishes)

    26 seasons

    Gwanar girki, fitacciya kuma mai gabatarwa, Fatima Gwadabe na zakulo abincin Arewacin Najeriya da za a iya girkawa a kowanne na’in dakin girki. Kowanne shiri kan kawo muku sabon girki daga Arewa, a gabatar da shi cikin nishadi, kuma cikin sauki mataki mataki. Baya ga koyar da girke-girke masu mah...

  • Daga Titi (Street Quiz)

    3 seasons

    Shirin "Daga Titi" Gajeren shirine na ban dariya wanda yake dauko tsofoffin kalmomin hausa, gagara gwari, tarihi na hausa dan a samu ko waye zai iya fada daidai a inda mai gabatar da shirin yake tambayar a kan titi.

  • Story Book (Having Fun Reading With Your Kids)

    2 seasons

    Wannan kirkirarran shiri ne da aka shirya shi domin Yara, don wayar musu da kai game da littafin tsatsuniyoyi a kuma dada jaddada wayar musu da kai a kan akidar nan ta shiga duniyar karance-karance da kuma karfafa tunaninsu. Ana gabatar da wannan shiri domin Iyaye su kalla tare da ‘Ya’yansu. A ko...

  • Alawar Yara (Sweets for Kids)

    7 seasons

    Alawar Yara” shiri ne domin yara da ma iyaye baki daya. Shiri ne da yake zuwa da labarai dake kunshe da darrussa da kuma sauran abubuwa domin yara. Cikin nishadi da ilmantarwa, labarun kan jawo hankulan yara masu kallo da kuma wadanda suka kasance a cikin shirin da suka zo daga makarantu, da kuma...

  • Tauraruwa (Women’s Role Model)

    10 seasons

    Wannan shiri mai zaburarwa na karfafawa mata matasa guiwa don su tashi tsaye su cimma manufofinsu, ko wanne irin kalubale za su iya fuskanta. Ta hanyar zakulo matan da suka yi nasara a rayuwarsu daga bangarori daban daban, Shirin tauraruwa yana zaburar da mata masu kallo son su kai ga nasara su z...

  • Amo Daga Arewa (Traditional Music From The North)

    1 season

    Shirin “Amo Daga Arewa” na tattaro muku shahararrun mawakan Hausa na gargajiya da na zamani daga Najeriya da yammacin Afirka da wani salon kida na musamman. Shirin kan tattaro makada da mawaka daban-daban wadanda suka yi fice daga dukkan bangarorin wakoki daban-daban baya ga salon gambara da na i...

  • Hip Hop (Top Artistes Profiles)

    13 seasons

    Hip Hop na zamowa wani bangare na musamman a wajen matasa ‘yan birni dake Arewacin Najeriya. Shirin “H Hip Hop” na tabo wannan fage na wake-wake. Mashiryin shirin nan na tashar AREWA24, mai gambarar da ya lashe lambar yabo, wato Nomiis Gee kan yi duba kan batutuwan bayan fage don tattaunawa da m...

  • Zafafa Goma (Weekly Countdown Show)

    29 seasons

    Ku kasance tare da shahararren mawakin Hip Hop din nan na tashar AREWA24 da ya lashe lambobin yabo, wato Nomiis Gee, a cikin shirin Zafafa 10 da ke zuwa kowanne mako, wanda ya kunshi wakokin manyan mawaka a Arewa da kuma al’ummar Hausawa dake kasashen ketare. Ya kan zo da bidiyon wakoki goma da ...

  • Sharhin Finafinai (Weekly Review of Top Movies)

    9 seasons

    Sharhin fina-finan Kannywood shiri ne da ke mai da hankali wurin kawo muku tattaunawa da bibiyar fina-finan Kannywood. Har ila yau, shirin na yin duba ga irin fina-finan da ake haskawa a gidajen cinema da wasannin kwaikwai ko kuma kura-kuran da ake tafkawa a yayin gudanar da shiri, hatta fina-fin...

  • Waiwaye (A Taste of Northern Nigerian Culture)

    9 seasons

    Wannan shiri an samar da shi ne don al’adu da mutane daban-daban na Arewacin Najeriya, inda yake mayar da hankali a kan harshe, da fasaha, da tarihi da kuma al’adun mutanen Arewacin Najeriya. Shirin “Waiwaye” kan yi nuni da al’adu da dabi’un masu tushe na Arewacin Najeriya, inda yake zagayawa dom...

  • Kundin Kannywood (Behind The Scenes In Kannywood)

    22 seasons

    Sanannen shirin Kundin Kannywood shiri ne da ke kunna nutso a cikin masana’antar shirya fina-finai ta Najeriya, wato Kannywood. Wanda daya daga cikin jaruman Kannywood mai farin jini ke gabatarwa, wato Aminu Shariff ma’aikacin tashar AREWA24. Shirin kundin Kannywood kan yi sharhi a kan sabbi da k...

  • Gari Ya Waye (AREWA24’s Top Rated Morning Show)

    21 seasons

    Shirin Gari ya waye na Tashar AREWA24 da ke zuwa a kullum yana duba ne ga dukkanin bangarori rayuwa a Arewacin Najeriya – Al’adu, tsarin rayuwa, matasa, al’amuran yau da kullum, nishadi da silima, lafiya da karfin jiki, dangantaka, sana’o’i, fasaha, jaruman fina-finai da dai sauransu. Shirin gar...

  • Gidan Badamasi (New Sit - Com Series)

    1 season

    Gidan Badamasi sabon fim din wasan barkwanci ne da ake dauki-ba-dadi a tsakanin wasu irin ‘ya’ya masu kunnen kashi da mahaifinsu Alhaji Badamasi. Badamasi dattijon attajiri dan kimanin shekaru saba’in ya yi aure-aure da dama a rayuwarsa, inda ya haifi ‘ya’ya masu yawan gaske, wasu ma bai san ina ...