Zabi Biyu

Zabi Biyu

0 Episodes

Wasu samarin dalibai a wata Jami’a, Don Nas attajiri da Mansur mai ji da kansa, sun Sanya wata kyakkyawar budurwa (Safiyya) a caca. Abin ya fara ne kamar wasa, daga musu, sai abu ya zama tashin hankali, inda Don Nas yace da Mansur in har yayi nasarar shawo kan soyayyar Safiyya ta amince za ta aure shi to zai ba shi sabuwar motarsa Marsandi sabon yayi. Tun daga wannan lokaci al’amura ba su sake kasancewa daidai ba ga wadannan samari, domin rayuwarsu ta shiga rudani, a cikinsu har da Bello, saurayin da aka sanya masa rana da Safiyya, kwanaki kadan suka rage a daura musu aure, bai san ashe an sanya amaryarsa Safiyya a caca ba.

Subscribe Share
Zabi Biyu