Wasan kwaikwayo ne da ya ke nuna tabarbarewar al’amura cikin rayuwarmu ta yau da kullum da kuma rayuwar ma’aikantan wutar lantarki wadanda ke da sa hannu wajen sace miliyoyin kudaden kamfani. Mallam Matazu da Mrs. Joy Lottana manyan ma’aikatan ne a kamfanin wutar lantarki wadanke su ke da sa hannu cikin munanan ayyukan magudi da cin miliyoyin kudaden kamfani ta hanyar samar da katin wuta na bogi da kuma jonawa kwastomomin wuta ba tare da bin ka’ida ba. Da sannu kamfani gano abun da yake faruwa kuma ya sanya aka fara bincike ta hanyar aika wani babban dan sanda cikin kamfanin yayi basaje a matsayin mai gadi dan aiwatar da bincike da gano ma su hannu a cikin harkokin rashawar. Sai a karshen binciken ne ake kama wasu manyan ma’aikatan kamfanin mutum biyu dumu dumu da laifi.
Up Next in Season One (1)
-
Short Film 2 | English
Wasan kwaikwayo ne wanda ya kunshi labarin wata makaranta da take fuskatar kalubale da bangaren rashin zuwa da guduwar dalibai daga makaranta sakamakon yawan faduwar jarrabawa. Haka ne ya sanya ma’aikatan makarantar su ka koma satar amsa a jarrabawa dan dalibansu su tsallake jarrabawa. Mr. Akasa ...
-
Short Film 3 | Hausa
Wasan kwaikwayo ne da ya ke nuna gwagwarmayar ‘yan jarida wajen yaki da rashawa cikin al’umma musamman ma ta bangaren karatu. A cikin labarin, wasu makarantun firamare ne na gwamnati na wata jiha guda uku suka rushe bayan gyaran gini da aka yi mu su. Inda dalibai su ka rasa rayukansu yayin da was...
-
Short Film 4 | English
Wani ma’aikacin kamfanin wutar lantarki ne tsundum cikin harkokin rashawa da karbar cin hanci daga wajen kwastomi ma su kokarin samun wuta ba tare da sun biya ba ko ta kaka. Wasan kwaikwayon ya kunshi harkokin rashawa na yau da kullum da ma’akatan lantarki ke aiwatarwa wadanda su ka hada da cin k...