Wasan kwaikwayo ne wanda ya kunshi labarin wata makaranta da take fuskatar kalubale da bangaren rashin zuwa da guduwar dalibai daga makaranta sakamakon yawan faduwar jarrabawa. Haka ne ya sanya ma’aikatan makarantar su ka koma satar amsa a jarrabawa dan dalibansu su tsallake jarrabawa. Mr. Akasa shi ne mataimakin shugaban makarantar, mutum ne wanda ya dade yana jan dalibansa a jiki yana koyar da su sanin ya kamata da amfanin yin karatu dan tsallake jarrabawa. Duk da zabin makarantar na samarwa da dalibanta amsar jarrabawa, sai daliban makarantar su ka rike amana su ka nuna sanin ya kamata su ka ki bada hadin kai da satar amsar jarrabawar duk da rashin kasancewar Mr. Akasa cikin makarantar a lokacin sakamakon rashin lafiya.
Up Next in Season One (1)
-
Short Film 3 | Hausa
Wasan kwaikwayo ne da ya ke nuna gwagwarmayar ‘yan jarida wajen yaki da rashawa cikin al’umma musamman ma ta bangaren karatu. A cikin labarin, wasu makarantun firamare ne na gwamnati na wata jiha guda uku suka rushe bayan gyaran gini da aka yi mu su. Inda dalibai su ka rasa rayukansu yayin da was...
-
Short Film 4 | English
Wani ma’aikacin kamfanin wutar lantarki ne tsundum cikin harkokin rashawa da karbar cin hanci daga wajen kwastomi ma su kokarin samun wuta ba tare da sun biya ba ko ta kaka. Wasan kwaikwayon ya kunshi harkokin rashawa na yau da kullum da ma’akatan lantarki ke aiwatarwa wadanda su ka hada da cin k...