Live stream preview
Short Film 3 | Hausa
28m
Wasan kwaikwayo ne da ya ke nuna gwagwarmayar ‘yan jarida wajen yaki da rashawa cikin al’umma musamman ma ta bangaren karatu. A cikin labarin, wasu makarantun firamare ne na gwamnati na wata jiha guda uku suka rushe bayan gyaran gini da aka yi mu su. Inda dalibai su ka rasa rayukansu yayin da wasu daliban da malamai da dama su ka tsira da rauni. Anan ne wani dan jarida ya daura damarar gano gaskiyar batun, inda ya tono wata harkalla ta rashawa da gwamnati ke bada kwantiragin na ayyukan ci gaba, da rashawa wajen aiwatar da ayyukan ci gaba da harkokin rashawa da ma’aikatan gwamnati ke aiwatarwa da kuma ware kudaden kudaden ayyukan ci gaba ba tare da aiwatar da su ba.