Short Film 1 | Hausa
15m
Wasan kwaikwayo ne da ya ke nuna tabarbarewar al’amura cikin rayuwarmu ta yau da kullum da kuma rayuwar ma’aikantan wutar lantarki wadanda ke da sa hannu wajen sace miliyoyin kudaden kamfani. Mallam Matazu da Mrs. Joy Lottana manyan ma’aikatan ne a kamfanin wutar lantarki wadanke su ke da sa hannu cikin munanan ayyukan magudi da cin miliyoyin kudaden kamfani ta hanyar samar da katin wuta na bogi da kuma jonawa kwastomomin wuta ba tare da bin ka’ida ba. Da sannu kamfani gano abun da yake faruwa kuma ya sanya aka fara bincike ta hanyar aika wani babban dan sanda cikin kamfanin yayi basaje a matsayin mai gadi dan aiwatar da bincike da gano ma su hannu a cikin harkokin rashawar. Sai a karshen binciken ne ake kama wasu manyan ma’aikatan kamfanin mutum biyu dumu dumu da laifi.