Kwana Casa'in Episode 7
54m
Kwana Casa’in wasan kwaikwayo ne da aka gina shi a kan tarka-tirkar siyasa da cin hanci da rashawa. Labarin yana faruwa ne a wani kirkirarren gari mai suna Alfawa. An fara labarin ne ana dab da fara zaben gwamna. Yakin neman zabe ya dauki zafi a lokacin da gwamna mai ci ya dage lallai ko ta halin kaka sai ya koma kan mulki duk kuwa da cewa bai yi wa talakawa wani abin kirki ba. Bangaren lafiya na daya daga cikin bangarorin da aka yi watsi da su, mutane na ta mutuwa a asibitocin gwamnati saboda rashin magani da kyakkyawar kulawa. ‘yan jaridu an sanya musu linzami ba a son su fadi gaskiya, yayin da abokan adawa kuma aka sanya takalmin karfe aka take su don gudun kada su yi tasiri. Haka nan an yi amfani da masu gidan rana wajen rufe bakin wasu daga cikin ‘yan hammaya. Dantakar da ya fi kawo barazana ga gwamna mai ci ya hadu da babban kalubale, zagon kasa da cin dunduniya, amma duk wannan bai hana shi ya kai labara ba sakamakon jajirtattun abokai na amana da suka mara masa baya. To sai kuma har kullum karshen wata matsalar, shi ne yake zamowa farkon wata sabuwar matsalar a nan gaba.