Live stream preview
Alawar Yara Zango Na 6 Kashi 8
25m
Alawar Yara” shiri ne domin yara da ma iyaye baki daya. Shiri ne da yake zuwa da labarai dake kunshe da darrussa da kuma sauran abubuwa domin yara. Cikin nishadi da ilmantarwa, labarun kan jawo hankulan yara masu kallo da kuma wadanda suka kasance a cikin shirin da suka zo daga makarantu, da kuma yaran da suke kallo a gida. Kowanne shiri yana karewa ne da ‘yar tattaunawa a kan darasin kowanne labari, da kuma wani abu da aka yi, kamar ziyartar gidan namun daji ko wata dama ga yara domin su zana abin da suke so.