So Sanadi
SO SANADI labarin rigima ce tsakanin ‘yan uwa biyu. Daya daga ciki ya dawo ne daga Turai da tasirin dabi’u da al’adu wadanda suka yi sabani da na kasarsa, kuma yana neman auren ‘yar kawunsa wadda ta riga ta samu tsayayye. Hakan ya jawo rikicin cikin dangin.