Gidan Badamasi (New Sit - Com Series)

Gidan Badamasi (New Sit - Com Series)

13 Episodes

Gidan Badamasi sabon fim din wasan barkwanci ne da ake dauki-ba-dadi a tsakanin wasu irin ‘ya’ya masu kunnen kashi da mahaifinsu Alhaji Badamasi. Badamasi dattijon attajiri dan kimanin shekaru saba’in ya yi aure-aure da dama a rayuwarsa, inda ya haifi ‘ya’ya masu yawan gaske, wasu ma bai san ina suke ba a halin yanzu. A wannan wasan kwaikwayo an fara kai ruwa rana ne daga lokacin da Alhaji Badamasi ya kasa cika alkwarin kudin da ya yi wa ‘ya’yansa. Yaki ya barke a tsakanin marowacin uba da hadamammun ‘ya’ya. Ba a taba yin fim kamar gidan badamasi a kasar hausa ba. Fim ne na barkwanci mai dauke da nishantarwa da ilmantarwa ta hanyar amfani da gwanayen ‘yan wasan barkwanci ta yadda mutum zai yi ta zura idanu yana jiran ganin abin da zai faru a nan gaba.

Gidan Badamasi (New Sit - Com Series)