Shirin Gari ya wayena Tashar AREWA24 da ke zuwa a kullum yana duba ne ga dukkanin bangarori rayuwa a Arewacin Najeriya – Al’adu, tsarin rayuwa, matasa, al’amuran yau da kullum, nishadi da silima, lafiya da karfin jiki, dangantaka, sana’o’i, fasaha, jaruman fina-finai da dai sauransu. Shirin gari ya waye ya hada da taattaunawa a dakin shirye-shirye da kuma rahotanni daga sassa daban daban da kuma wasu bangarorin shirin.
Ku kasance tare da shahararren mawakin Hip Hop din nan na tashar AREWA24 da ya lashe lambobin yabo, wato Nomiis Gee, a cikin shirin Zafafa 10 da ke zuwa kowanne mako, wanda ya kunshi wakokin manyan mawaka a Arewa da kuma al’ummar Hausawa dake kasashen ketare. Ya kan zo da bidiyon wakoki goma da s...